Hukumar Yan Sanda Sun Kama Mutun Uku Bayan Ganin Gawar Mutun 20 a…

Rundunar yan sandan Najeriya sun kama mutum uku wanda ya kasance duka maza bayan gano gawar mutane 20 da aka kyafe su a kusa da birnin Benin na Jihar Edo dake kudancin Nigeria.
An yi nasarar gano gawarwakin ne a wani gini da ake kyautata zaton ana amfani da shi domin yin tsafin Voodoo a jihar ta Edo.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor, ya shaida wa Edunoz .com cewa gawarwakin na maza 15 ne da kuma mata mutum uku da kananan yara guda biyu.
Kawo yanzu hukumar yan sandan ba ta tabbatar da tsawon lokacin da kyafaffun gawarwakin suka ɗauka ba a ginin da lokacin da aka kashe su.
Nwabuzor ya kara da cewa ‘yan sanda da ‘yan kato da gora ɗauke da makamai ne suka kai samame ginin da ke wajen birnin bayan wani ya tsegunta musu halin da ake ciki.
Maƙwabtan ginin da aka gano gawarwakin sun kaɗu suna mamakin yadda aka ɓoye su a wurin ba tare da wani ya sani a cikin su ba.
Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Avonoren.Com.