Labaran Hausa

Toffa` Bello Turji Shugaban Yan Ta’addan Boko Haram Yanzu Yayi Na…

Al’ummar kasar Najeriya na ci gaba da Allah-wadai tun bayan fitowar wasu bayanai kan fitaccen ɗan bindigar nan wato Bello Turji Kachalla da ake cewa ya rungumi sulhu bayan tabbatar da tubansa.

A ranar Lahadi ne gwamanatin Zamfara ta fitar da wata sanarwa da ke cewa fitaccen ɗan bindigar ya tuba, kuma ya rungumi zaman lafiya bayan ya shafe shekaru ya na garkuwa da mutane da kashe na kashewa.

Sai dai wannan labari ya zo wa galibin ‘yan kasar da ke ɗiga ayar tambaya da mamaki, inda galibin mutane har a shafukan sada zumunta ke tafka muhawara da nuna shakku kan tuban Bello Turji.

Mataimakin gwamanan Jihar ta Zamfara ne ya gabatar da sanarwar game da mutumin da yawancin mutane a arewacin Najeriya ke kiransa da ‘Sarkin ‘yan Ta’adda.

An dai shafe shekaru jami’an ‘yan sanda na nemansa ruwa-a-jallo domin laifukan ta’addancin da ake tuhumarsa da aikatawa a jihohin Zamfara da kuma Sokoto da Katsina da kuma masu makwabtaka da wadannan garuruwa.

Wannan ne ya sa awancin mazauna jihar ta Zamfara ke bayyana shakku bayan da suka sami labarin tuban Bello Turji.

Bello Turji

Sun riƙa bayyana rashin amincewarsu da wannan labarin inda wasunsu ke cewa ɗan bindigar ba abin da za a amince da shi ne ba.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button