World News

Qalu Innalillahi Yan Bindiga a Katsina Sun Sace Matafiya da Ba’asan Adadin Suba….

Wasu ‘yan bindiga a jihar Katsina da ke arewacin Nigeria da ba’asan ko suwane ba ,sun sace matafiyan da ba a san adadinsu ba a kan hanyar Katsina zuwa Jibia.

Wasu mazauna wurin da lamarin faru, sun shaida wa Edunoz cewa ‘yan bindigar sun isa wurin ne a kan babura kuma sun rika yin harbin kan mai-uwa-da-wabi, al’amarin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku da kuma raunata wasu fasinjojin da dama.

WOLD NEWS

Wannan lamarin dai ya faru ne a daidai kauyen Kadobe, kusa da wani wuri da ‘yan sandan kwantar da tarzoma suka kafa shingen bincike.

Da da misalin karfe biyar na yammacin Lahadi ‘yan bindigar suka kai hari wajen,amma kuma wasu matafiyan sun samu dama sun tserewa yan bindigar.

Mazaun yankin na Jibia dai na koka wa kan karuwar hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa kan matafiya da mazauna karamar hukumar lamarin da suka alakanta da hijirar da ‘yan bindigar ke yi daga jIhar Zamfara mai makwabtaka saboda abin da suka kira “sulhun da gwamnatin Zamfarar ke yi da ‘yan bindiga a jihar.

Sun kuma ce wannan lamarin ya fi karfin gwamnatin Katsina, saboda haka suke bukatar gwamnatin tarayya da ta dauki karin matakan inganta tsaro a yankin.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Avonoren.Com.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button