Malam Ibrahim Shekarau Ya Dawo Jam’iyar PDP Bayan Ya Tashi Daga NNPP Yanzu….

Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan majalisar dattawa Malam Ibrahim Shekarau ya koma jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ‘yan watanni kadan bayan komawarsa jam’iyyar NNPP.
Wata majiya mai karfi da ke da kusanci da tsohon gwamnan ta shaida wa Edunoz cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar wa Shekarau da tsare-tsarensa kuma shekarau din ya amince da su.
A ranar Litinin ne ake sa ran Atiku zai isa birnin na Kano don tattaunawa da tsohon gwamnan kano Shekarau, inda a lokacin ne kuma zai karɓe shi zuwa PDP a hukumance.
Shekarau ya ɗauki matakin komawa PDP sakamakon abin da ya kira “rashin adalci” da Rabiu Kwankwaso ya yi musu, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam’iyyar NNPP.
“Gaskiya ne mun shirya tsaf don tarɓar Atiku a Kano don su nemi hannun Malam bayan Shekarau ya yi wa majalisar Shura bayanin halin da ake ciki a NNPP,” a cewar majiyar.
Atiku zai je Kano tare da Shugaban PDP na Ƙasa Iyorchia Ayu da sauran jiga-jigan jam’iyyar adawa PDP.
Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.