Labaran Hausa

Malaman Jami’oi A Nigeria da ake Kirada ASUU Ta Yanke Shawarar Zata Kara Tsawaita Yajin Aikin Datake Gudanar Wa Yanzu…..

Ƙungiyar malaman jami’oi a Najeriya, da ake kira ASUU ta yanke shawarar zata kara tsawaita yajin aikin da take gudanarwa tsawon wata shida.

Jaridar Punch ta rawaito cewa wannan matakin ya zo ne bayan wata zazzafar tattaunawa da aka yi ranar Litinin ashirin da tara ga watan Augustan shekararnan game da yadda za a cimma matsaya tsakanin ƙungiyar da kuma gwamnati.

An ɗauki matakin ci gaba da yajin aikin bayan ganawar kwamitin zartarwa a hedikwatar ASUU da ke Jami’ar Abuja, babban birnin kasar taNajeriya.

Ƙungiyar ASUU dai ta shafe watanni yawa tana gudanar da wannan yajin aikin da ya tilastawa ɗaliban jami’oin gwamnati zama a gida.

ASUU na ganin gudanar da yajin aikin ne don hanyar samun mafita ga tarin buƙatun da ta gabatar wa gwamnatin Najeriya ciki har da batun inganta musu albashi.

Mutane da yawa suna kokawa akan yajin aikin sakamakon sun bata lokuta masu yawa, mutanan na cewa wannan yajin aiki ya dakile musu rayuwa su basuje makaranta ba kuma su basu sami wata mafita ba, saboda kullum tunanin su gobe za’a koma makaranta.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Avonoren.Com.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button