Labaran Hausa

Innalillahi Wainna Ilaihi Rajiun` Bene Mai Hawa You Yafada Kan Mutane a Kasuwar….

An yanzu ne aka kammala aikin ceto a wajen da wani bene mai hawa uku ya rushe a kasuwar beirut da ke Jihar Kano – inda gini ya danne mutane da dama

Jami’an agajin gaggawa sun ce mutum daya ya mutu a baraguzan gini yayin da bakwai kuma suka samu raunuka, inda aka garzaya da su zuwa wani babban asibiti domin basu kulawa da ta dace.

Sai dai hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta ce daya daga cikin wadanda suka samu raunuka ya samu karaya kuma yana asibiti ana kula da shi.

Hukumar ta NEMA ta fadawa Edunoz cewa ta kammala aikin ceto zuwa yanzu kuma babu sauran mutane da ke karkashin baraguzan gini.

Benen wanda yake dauke da shaguna da dama ba a kammala gina shi ba kafin ya rushe a jiya Talata. Ba a dai san me ya haddasa rushewar ginin ba.

Ana yawaita samun rushewar gine-gine a biranen Najeriya da ke janyo asarar rayuka, inda sau da dama ake dora laifin hakan a kan rashin bin ka’idojin gini da mutane basa bi.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Avonoren.Com.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button