Babbar Magana Hukumar EFCC Ta Sanar da Cewar Tana Neman Dan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya Na APC Wato A.A Zaura Ruwa A Jallo……….

Hukumar da ta ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Nigeria ta bayyana neman dan takarar Sanata na Kano ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar APC, AbdulKareem AbdulSalam Zaura wanda jama’a suka fi sani da A.A Zaura.
Babban lauyan hukumar ta EFCC, Ahmad Rogha ne ya bayyana haka ne ga manema labarai a ranar Litinin bayan da aka dawo da batun shari’ar dala miliyan 1.3 da ake yi wa Dan takarar A.A Zaura a babbar kotun tarayya da ke jihar Kano.
Duk da kasacewa shari’ar da aka shirya yi wa dan takarar ba ta samu ba, saboda rashin halartar alkalin da ke sauraron shari’ar, wanda aka ce yana halartar wani taron kasa a wajen birnin jihar ta Kano.
Haka zalika lauyan na hukumar ta EFCC ya bayyana cewa ya kamata Dan takarar A.A Zaura ya kai kansa ga hukumar ta EFCC.
“Ga Maganar tasa”
“Muna neman dan takarar sanata na kano ta tsakiya wanda akafi sani A.A Zaura kuma za mu kama shi da zarar mun same shi”.
”A ka’ida, ya kamata a ce zuwa yanzu yana hannunmu domin kuwa kotu ta tabbatar mana da haka, amma ina tabbatar da cewa za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu a zamanta na gaba wanda za’ai ranar 30 ga Janairun shekarar 2023”.
Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarin Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Avenoren.Com.