Cristiano Ronaldo Shine Mutumin Dayafi Kowa Yawan Magoya Baya A Kafofin Sada Zumunta Amma Har Yanzu Baice Komai Ba Game Da Nasarar Da Lionel Messi Yasamu Ba……………

Dan Wasa Cristiano Ronaldo, shine mutum na farko da yafi kowa magoya baya a shafukan sada zumunta, kawo yanzu bai ce komai ba, tun bayan da Dan Wasa Lionel Messi ya taimaki Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 a Qatar.
Kasar Argentina ta samu nasara a kan kasar Faransa da ci hudu da biyu a bugun daga kai sai gola bayan sun buga wasa har na tsawon mintina 120 kuma aka tashi uku da uku.
Masoya kwallon kafa na duniya sun tabbatar da cewa ba a taba buga wani wasa wanda ya kayatar kamar wannan ba a tarihin gasar cin kofin duniya.
Dan Wasa Cristiano Ronaldo wanda magoya bayansa miliyan 780 ne jumlace a shafukan Twitter da Instagram da kuma Facebook, ya yi gum da bakinsa baice komai ba game da nasarar Argentina da Messi ya samu ba.
Ku Kalli cikakken videon ?
Muna Matukar godiya a gareku mai tarin yawa tare da fatan alkairi sakamakon ziyartar wannan gida namu mai albarka kuci gaba da bibiyar wannan gidan labarai na Avonoren.com